Category Archives: News Headlines

Akwai bukatar nada ministan lura da ma’aikatar lantarki na daban

  Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ta nada wani Ministan lura da ma’aikatar lantarki na daban don inganta harkokin lantarki a kasar nan. Rahotanni sun bayyana cewa karkashin gwamnatin yanzu, an sanya bangaren ma’aikatar lantarki karkashin ma’aikatar ayyuka da gidaje. Haka zalika majalisar dattawan ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da motoci…

Read more

zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari

Gwamnatin Najeriya ta ce zata sake nazartar sayar da kadarorin gwamnati da suka shafi bangaren samar da wutar lantarki da nufin sake fasalin ikon mallakar kamfanonin wanda hakan a cewar ta zai taimaka wajen bunkasa samar da wutar lantarkin kasar. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bayyana hakan lokacin da yake bayani yayinwani taro kan…

Read more

Shugaba Buhari ya aikewa majalisar Dattawa wasikar amincewa da Aisha Ahmad

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa da majalisar Dattawa wasikar neman amincewa da Aisha Ahmad a matsayin mataimakiyar gwamnan babban bankin kasa na CBN. Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mashawarcin shugaban kasa na musamman kan kafofin yada labarai Femi Adesina ya fitar yau a birnin tarayya Abuja. Sanarwar ta bayyana cewa ana…

Read more

Hukumar WAEC ta ce na’urorin zamani na saukakawa ayyukan hukumar

Hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandare ta yammacin afurka wato WAEC, ta ce, na’urori na zamani irinsu wayoyi kirar smartphone da kafafen sada zumunta na internet suna matukar saukakawa masu satar jarabawa wajen gudanar da haramtattun ayyukansu. Shugaban hukumar ta WAEC Iyi Uwadiae ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a wani bangare…

Read more

tunein

Tune In
Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO