Listen – iOS

A Yau Za’a Gudanar Da Zaben Hukumar Kwallon Kafa Ta Nahiyar Afrika

Alhamis din yau ne za a zabi shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afirka, CAF wanda shugaban hukumar mai ci, Issa Hayatou da Ahmad Ahmad dan kasar Madagascar suke takara.

Za dai a gudanar da zaben ne a babban birnin kasar Habasha, watau Adis Ababa tsakanin mutanen biyu.

Shugabanni biyar kawai CAF ta yi tun da aka kafa ta shekaru 60 da suka gabata, kuma rabon ta da samu wani sabon shugaba tun 1988.

Masana harkokin kwallon kafa na hasashen cewa zaben na ranar Alhamis na iya kawo sauyi a hukumar, amma kuma ba a taba samun wanda ya kalubalanci shi Issa Hayatou ba a baya ba tare da ya sare ba kafin lokacin da za a gudanar da zabe.

A gasar Premier ta kasa da aka gudanar jiya, Enyimba ta yi nasara kan FC Ifeanyiu Ubah da ci 2-0. Yayin da wasa tsakanin MFM da Wikki Tourist aka tashi da ci 1 da 1.

A wasannin sada zumunci da ke gudana a birni Kano da kewaye kuwa, yau New Boys Kofar-Waika za ta fafata da Dortmund, Rijiyar Zaki a filin Dortmond da ke Rijiyar Zaki.

A gasar kofin Yurofa, wasanni da za a buga tsakanin:

Man Utd da CF Rostov, sai kuma Besiktas da Olympiakos,

yayin da FK Krasnodar za ta fafata Celta Vigo, inda

Roma za ta kece raini da Lyon.

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO