Listen – iOS

Majalisar Dattijai da Bangaren zartarwa Suyi Duba Kan Batun Tabbatar Da Ibrahim Magu

 

An bukaci Majalisar Dattijai da bangaren zartarwa na Tarayya da su garzaya kotu domin neman fassara dangane da ikon tabbatar da Shugaban hukumar nan mai yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC kasancewar kundin tsarin mulkin kasar nan bai ce komai ba game da batun.

Tsohon Shugaban kungiyar Lauyoyi ta kasa reshen Kano Barista Abdulrazaq Aikawa ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da shi a cikin Shirin Mu Leka Mu Gano na musamman nan gidan Rediyon Freedom wanda ya maida hankali kan kin tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin Shugaban hukumar ta EFCC.

Barista Abdulrazaq Aikawa ya shaida cewa kamata ya yi a warware matsalar bisa doron doka a maimakon bin matakan Siyasa.

Ya kuma kara da cewa rashin tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin Shugaban EFCC da majalisar Dattijai ta yi ya nuna cewa akwai sabanin ra’ayi a fadar Shugaban kasa dangane da wannan al’amari.

Rahotanni sun bayyana cewa fadar Shugaban kasa ta sanar da cewa har ya zuwa yanzu ba ta karbi wani sako a hukumance da ke daga majalisar Dattijai da ke nuna dalilansu na kin amincewa da Ibrahim Magu a matsayin Shugaban EFCC ba.

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO