History Trivia

A ranar 21 ga watan Agustan shekarar 1993 aka kafa hukumar kwallon faka ta tarayya

An samu Sabani Tsakanin Kyaftin Din Kano Pillars Da Kocinsa

An samu sabanin ra’ayi tsakanin kyaftin din kungiyar Kano Pillars Rabiu Pele da mai horas da kungiyar Khadiri Ikhana a bangare guda kuma da magoya bayan kungiyar sakamakon yunkurin da Kocin na Pilars ya yi na cire dan wasan gaban kungiyar Musa Najere tun a Zangon farko.

Rahotonni sun ce, kyaftin din Pillars Rabiu Pele ya ki amincewa da a sauya dan wasan gaban, yayin da a lokaci guda magoya bayan kungiyar su ka fara shewa na nuna rashin amincewa da matakin.

Lamarin dai ya faru ne a jiya Lahadi yayin fafatawa da Pillars ta yi da takwararta ta Gombe United a gasar premier.

Daga bisani dai an sasanta inda har Musa Najere  ya zura kwallaye biyu da Pillars ta ci a ragar Gombe United.

a sauran sakamakon wasannin firimiya da aka gudanar a jiya kuwa –

Ifeanyi Uba United 3- yayin da El- kanemi Warriors na 2

Lobi Stars na da 0- Nassarawa United 0

Niger Tornadoes 1- Akwa United 0

Shooting stars 0 – Abia Warriors 0

Wikki Tourist 2- Katsina United 1

MFM FC   2- Plateau United  1

A firimiyar Ingila

Tottenham  Hotspur 2   SouthHampton 1

Middlesbrough 1     Manchester United 3

Manchester city 1  Liverpool 1

A Seriar Italiya

Empoli 2 Napoli 3

Atalanta 3 Pescara 0

A laligar Spain

Barcelona 4 Valencia 2

 

 

 

 

 

 

tunein

Tune In