Listen – iOS

Cutar Gaulantaka

 

Cutar gaulantaka cuta ce da take shafar kwayoyin halitta da kan yi wa yara illa tun suna mahaifa, kafin su zo duniya inda ake haifar su da wata irin halitta daban da ta sauran yara ba.

A wata tattaunawa da rediyon Freedom ta yi da wata mai kula da yaran da ke fama da ciwon, Malama Samira Sunusi Hamisu ta bayyana cewa suna na da wuyar sha’ani musamman wajen kula da da su, ko kuma mu’amalar su da suran yara.

Malamar wadda ta yi wannan bayani ne kan yadda mu’amala da yaran take ne a wani bangare na bikin ranar yara masu fama da ciwon gaulantaka ta duniya ta bana wadda ake gabatrawa a yau.

Yaran da ke fama da ciwon da muka zanta da su sun bayyana irin kalubalen da suke fusksnta da kuma kokarin da suke yin a yin wata sana’a tare da irin burace-buracen da suke da shi a rayuwa.

Ita shugaba ma shugabar sashin kula da kananan yara na asibitin kwararru na Murtala da ke nan Kano, Dokta Safiya Gambo bayyana irin abubuwan da ke kawo wannan matsala da kuma hanyoyin kare haihuwar yara masu irin wannan larura ta yi.

Wakiliyar mu Rukayya Abba Kabara ta rawaito cewa taken bikin na bana shine ‘’Muryata A Cikin Al’ummata.’’ wanda hakan yake nufin bawa irin waddannan yara damar yin Magana cikin al’ummar su sannan kuma a suraresu tare da kawo musu daukin gaggawa.

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO