Listen – iOS

Matsalolin Tattalin Arzikin Nijeriya Na Da Nasaba Da Abinda Gwamnati Ta Gada

Wasu masana harkokin tattalin arziki sun bayyana matsalar da kasar nan ke fuskanta a wannan bangare da cewa, gwamnatin Tarayya ta gaji matsalar ne daga shugabannin baya, sakammakon rufe masana’antu, da durkushewar su, da kuma dogaro kan kudin da a ke samu daga man fetur.

Mataimakin shugaban kungiyar masu masana’antu ta kasa, reshen jihar Kano, Ali Safiyanu Madugu, ya bayyana haka Litinin din nan, a shirin Freedom Radio na ‘Duniyar mu a Yau’, inda ya kara da cewa, galibin kasafin kudin da gwamnatoci ke yi ma ba a aiwatar da shi.

Alhaji Safiyanu, ya kuma ce, Nijeriya na da albarkatu masu dimbin yawa, amma kusan gwamnati ta dogara kacokan kan man fetur, alhali kuma kasa ba ta samar da shi yadda zai wadaci kowa; sa’an nan ga shi farashin man ya fadi a kasuwar duniya, ga kuma rashin tattalin kudi, wato tanadi domin gobe.

A na shi tsokaci, Ferfesa Garba Ibrahim Sheka, na Jami’ar Bayero, ya alakanta matsalar tattalin arzikin ga rashin bayar da fifiko kan kayayyakin da ake samarwa a gida, da kuma kwadayin samun kazamar riba, ya na mai cewa, har yanzu gwamnati ba ta fara daukar matakan fita daga wannan halin koma-baya da tattalin arziki ke ciki ba, domin akwai bukatar mayar da hankali kan ayyukan noma, da hakar ma’adinai, da kuma janyo hankalin masu zuba jari a bangaren masana’antu daga kasashen ketare.

Cikin shirin na Duniyar mu a Yau dai, kusan daukacin wadanda a ka tattauna da su, sun shawarci gwamnati ta kirkiro sababbin dabarun bunkasa tattalin arziki, da kuma rage shigowa da kayan amfani na yau da kullum, daga kasashen waje.

Sun kuma bukaci gwamnati ta fitar da wani tsari, da zai samar da tallafi ga masu masana’antu, domin samun daidaito, tare da samar da wadataccen makamashi, da ya hada da lantarki da man fetur, da iskar gas, domin farfado da masana’antun kasar nan.

 

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO