Listen – iOS

Kungiyar TUC Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Tayi Bayanin Kudaden Paris Kulob

Gamayyar kungiyoyin kwadago TUC Litinin din nan ta bukaci gwamnatin Tarayya da ta fayyace ayyukan da gwamnatocin jihohi za su yi da kasonsu na kudin ‘Paris Kulob’ da za a ba su.

TUC ta ce ta hakan ne za a yi maganin yadda gwamnatocin jihohin ke yin gaban kansu bayan sun karbi kudaden.

Gamayyar kungiyoyin kwadagon ta ce idan gwamnati ba ta fayyace  musu ayyukan da za su yi ba, to kuwa babu makawa abin da ya faru da Naira miliyan dubu 388 da aka ba su cikin watan Disamban bara, shi zai sake faruwa.

Cikin wata sanarwa da shugaban gamayyar kungiyoyin kwadagon kwamared Bobboi Kaigama da babban sakatarenta kwamared Musa Lawal Ozidi suka sanya wa hannu, TUC ta ce idan har ba a tsara wa gwamnonin yadda za su yi da kudin ba, to kuwa nan ba da jimawa ba za su sake daukan kokon barar neman karin tallafin kudi.

A satin da ya gabata ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci Ministar kudi da kuma Gwamnan babban bankin kasa, su bai wa jihohin 36 Naira miliyan dubu 500 na biyan bashin Paris Kulob, wanda gamayyar kungiyoyin kwadagon ke ganin cewa da a ce gwamnonin sun jalauta kason farko da aka ba su, hakika da rayuwa ta kyautata ga ‘yan Nigeria.

 

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO