Listen – iOS

Kungiyar kwallon kafa ta Katsina United ta ‘yan kasa da shekaru 15 ta casa takwararta ta Kano Pillar

Kungiyar kwallon kafa ta Katsina United ta ‘yan kasa da shekaru 15 ta casa takwararta ta Kano Pillars da ci uku da nema a gasar cin league ta kasa ta ‘yan kasa da shekaru 15.

 

Wakilinmu na fagen wasanni Abdullahi Isah ya ruwaito cewa Abdulkadir Yahaya da Yahaya Ahmed da kuma Suleiman Shehu ne suka cwa Katsina United kwallayen ta uku rigis.

 

Sauran sakamakon wasanni kuma ita ma kungiyar  Lobi stars ta sha kashi a hannun Nassarawa United da ci uku da nema a wasan da sukayi a filin wasa na fifa goal project da ke Abuja. Elkanemi warriors da Gombe United sun tashi a wasa da ci daya da daya, Niger Tornadoes da Plateau united sun yi canjaras da ci biyu da biyu.

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO