Listen – iOS

Hukumar EFCC ta gudanar da bincike a gidajen wasu tsofaffin gwamnoni biyu

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gudanar da bincike a gidajen wasu tsofaffin gwamnoni biyu, a ci gaba da binciken da take yi game da naira biliyan 13 da ta samu a dogon ginin Osborne Towers da ke unguwar Ikoyi a jihar Legas.

Gwamnonin da hukumar ta gudanar da binciken a gidajen nasu sun hadar da tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi, da kuma tsohon gwamnan jihar Bauchi kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP ta kasa, Ahmad Adamu Mu’azu.

Sauran fitattaun ‘yan Najeriya da ke zaune a dogon ginin da hukumar ta kai samame sun hadar da: tsohuwar shugabar kamfanin samar da man fetur na kasa NNPC, Misis Esther Nnamdi-Ogbue, da kuma mai gidan talabijin na Ebony Life Mista Mo Abudu.

Wata majiya daga hukumar ta EFCC ta bayyana cewa, hukumar ta gudanar da binciken ne dukkannin lunguna da sako na gidan duk kuwa da cewa babu mai zama a cikin su.

A cewar majiyar hukumar na zargin cewa ana iya ajiyar wasu kudaden a wasu bangarori na gidan da babu kowa a ciki.

Mashawarcin tsohon gwamnan na Anambra ta kafafen yada labarai Valentine Obinyem, ya tabbatar da cewa hukumar ta gudanar da binciken a gidan tsohon gwamnan cikin wata sanarwa da ya fitar.

 

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO