Listen – iOS

Mutane 745 ne suka rasa rayukansu sanadiyar cutar Sankarau

Gwamnatin Tarayya ta ce akalla mutane 745 ne suka rasa rayukansu tun bayan bullar cutar sankarau a kasar nan. Ha kuma mutane dubu takwas da hamsin da bakwai ne suka kamu da cutar a fadin kasa baki daya.

 

Ta ce komai ya gama kankama domin shawo kan yaduwar cutar a jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina da Kebbi da kuma Niger wadanda sune jihohin da lamarin yafi kamari.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bada shawara ga cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasa Dakta Lawal Bakare ya fitar jiya, yana mai cewar, daya daga cikin dabaru da ake bi domin shawo kan cutar ita ce wayar da kan jama’a gameda illar cutar a dukkannin fadin kasar nan.

 

Ya kara da cewa, sarakunan gargajiya da ke karkashin Inuwar sarakunan gargajiya masu kula da harkokin lafiya a matakin farko sunyi wani taro da gwamnonin arewa.

 

Ya ce taron wanda aka yi da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya ta kasa da kuma hukumomin da ke karkashinta da kuma abokan hulda na kasa da kasa da nufin shawo kan cutar.

 

Dakta Bakare ya kara da cewa alkaluman da suka tattara a ranar sha bakwai ga watan Aprilu akalla mutane dubu takwas da hamsin da bakwai ne suka kamu da cutar, inda 230 daga ciki an tabbatar da su a dakin bincike, yana mai cewar 745 daga ciki sun mutu.

 

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO