Listen – iOS

Hukumar shiryar gasar Olympic ta kasa zata kawo sauye sauye

Hukumar shirya gasar Olympic ta kasa NOC ta shirya kawo sauye sauye a dokokin zabe na hukumar don ganin anyi zaben ba tare da samun matsala ba.

Hakan dai ya biyo bayan takaddamar da ta faru a cikin hukumar wasanni ta kasa dangane  da dambarwar da ta taso akan zaben na hukomi daban dabam na wasanni a kasar nan da suka dakatar da wasu jami’an hukumomin tsayawa takara.

Wakilin mu Aminu Halilu Tudun Wada, ya ruwaito man cewa a baya bayan nan dai  hukumar shirya gasar Olympic ta duniya ta OIC ta yi barazanar korar kasar nan daga cikin hukumar matukar dambarwar ta ci gaba da faruwa.

A baya dai a cikin dokokin da aka saka sun hana shugaban hukumar Olympic ta kasa Habu Gumel tsayawa takara, da shugaban wasannin guje guje da motsa jiki na kasa Solomon Ogba, da shugaban hukumar wasannin Tennis ta kasa Sani Ndanusa, sai shugaban hukumar kwallon Kwando ta kasa Tijjani Umar.

A wasanni da suke gudana a birnin Kano da kewaye:

Idan muka koma bangaren Tennis kuma, yar wasa Serena Williams ta  bayyana cewa ta na dauke da juna biyu mako 12 bayan lashe gasar Grand Slam da ta yi.

Mai shekaru 35 Williams ta bayyana hakan ne a shafin ta na sada zumunta na snapchat, kafin daga baya ta goge hakan.

In Muka leka kwallon zari ruga ta Rugby, mai horas da kungiyar kasar Ingila Eddie Jones, ya bayyana sunan ‘yan wasa 15 da basu taba bugawa kasar wasa ba a cikin tawagar mutum 31 da za ta tunkari kasar Argentina a fafatawar da za su yi..

Dan was Dylan Harley shine zai jagoranci kungiyar a matsayin Kyaftin din ta..

A gasar cin kofin zakarun nahiyar turai da aka  fafata a daren jiya Barcelona ta fice daga gasar bayan kasa kai bantenta sakamakon kasa rama kwallon uku da ta kwasa a hannun abokiyar karawarta da Juventus,  awasn farko makon da ya wuce, wasan dai an tashi canjaras.

Ya yin da a gefe daya Monaco ta sanmu damar tsallakawa zuwa wasan kusa da na karshe bayan doke Brussia Dortmund, da ci 3 da 1.

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO