Listen – iOS

Akwai yiwuwar hukumar EFCC za ta bincike Goodluck Jonathan

Ana saran kwamitin fadar shugaban kasa mai bincike kan kudaden nan Naira biliyan 13 da aka samu a wani gida can a jihar Lagos zai tuhumi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da Gwamnan babban bankin kasa CBN da mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu.

Kwamitin zai kuma tuhumi dakataccen darakta Janar na hukumar leken asiri ta kasa Ayodele Oke da kuma wanda ya gabace shi wato Olaniyi Oladeji.

Haka kuma ana saran mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Manguno wanda shima Mamba ne a kwamitin zai yiwa kwamitin takaitaccen bayani dangane da abin daya sani kan rahoton da dakataccen darakta Janar na hukumar leken asiri ta kasa ya bashi dangane da sumamen daya kai ga gano kudaden.

Wata sanarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fitar ya nada mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci kwamitin binciken yayin da Atoni Janar kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami da mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro Babagana Manguno za su kasance mambobin kwamitin.

Kafa kwamitin dai ya biyo bayan, dakatarwar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa Sakataren gwamnatin Tarayya Injiya Babachir David Lawal kan batun kudaden nome ciyawa a yankin arewa maso gabashin kasar nan da kuma darakta Janar na hukumar leken asiri ta kasa Mr Ayodele Oke kan batun Naira biliyan 13 da aka gano a jihar Lagos.

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO