Listen – iOS

Hukumar INEC ta fara shirye-shiryen fito da sabbin hanyoyin zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yanke shawarar fara shirye-shiryen ci gaba da rajistar zabe a kasa baki daya daga ranar Alhamis mai zuwa 27 ga watan da muke ciki na Aprilu.

Ana dai zaran hukumar zata fara gudanar da ci gaban aikin rajistar zaben da kwamishinonin zabe guda uku kacal duba da yadda majalisar Dattijai ta gaza tabbatar da sunayen kwamishinonin 27 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike mata don tantancewa.

A wata sanarwa da kwamishinar hukumar ta kasa kuma mai rikon mukamin shugabar sashen bayanai na hukumar Amina Zakari ta fitar jiya Laraba, ta ce matakin ya biyo bayan wata ganawa ta musamman da kwamishinonin hukumar da sakatarorin mulkin hukumar na jihohin kasar nan 36 da birnin Tarayya Abuja suka gudanar.

A cewar Sanarwar, tattaunawar da jami’an hukumar ta INEC suka yi ta mai da hankali ne kan sabbin hanyoyi da dabarun da za a yi amfani da su yayin fara aikin rajistar masu kada kuri’ar baya ga tsayar da ranar da za a fara aikin.

Sanarwar ta ce, za a fara gudanar da ayyukan a ilahirin kananan hukumomin kasar nan 774 kuma a dukkanin ranakun aiki wato daga Litinin zuwa Juma a tun daga misalign karfe 9 na safe zuwa 3 na yammaci.

Ta ce hakan zai baiwa ‘yan najeriyar da shekarunsu bai kai minzalin yin rajistar a wancan lokaci ba damar yin rajistar da za su kada kuri’u da su, haka kuma wadanda suka yi rajistar a wancan lokaci da ba su karbi katin kada kuri’ar su ta din-din-din ba za su iya karba a yanzu.

Ta kuma shawarci ‘yan najeriyar da ke da rajistar kada kuri’ar da kada su kara zuwa wurin rajistar domin yin hakan babban laifin ne a tanadin kundin tsarin hukumar ta INEC.

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO