Listen – iOS

Ministoci uku sun gana da Muhammadu Buhari

Wasu ministoci guda uku sun gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari inda suka yi masa bayani kan ayyukan da ma’aikatun su ke gudanarwa.

 

Ministocin da aka ga fuskokin su a fadar shugaban kasar sun hadar da Kayode Fayemi na ma’adanai da Usani Usani na yankin Neja Delta da kuma Solomon Dalung na wasanni.

 

Da yake ganawa da manema labarai bayan kammala ganawarsu da shugaba Buhari cikin sirri, Kayode Fayemi ya ce sun yiwa shugaban karin haske kan abubuwa da dama game da ma’aikatun nasu.

 

 

Ya ce daga cikin abubuwan da suka sanar da shugaban akwai batun kudin nan Dala Miliyan 150 da bankin duniya ya amince ya bawa Najeriya da kuma wasu muhimman al’amura da suka shafi ma’aikatar sa.

 

Ya kuma ce ya sanar da shugaba Buhari game da batun hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba da kuma hanyoyin da za a magance matsalar.

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO