History Trivia

A ranar 21 ga watan Agustan shekarar 1993 aka kafa hukumar kwallon faka ta tarayya

An nada Dr Habibat Lawal a matsayin Mukaddashiyar Sakataren gwamnatin Tarayya

 

Ofishin shugaban kasa ya sanar da nadin Dr Habibat Lawal a matsayin Mukaddashiyar Sakataren gwamnatin Tarayya, bayan da Muhammadu Buhari ya dakatar da Mr Babachir David Lawal a jiya Laraba.

Sanarwar da ofishin ya bayar a yau, ta kuma bayyana nadin Jakada Arab Yadam, a matsayin mai rikon mukamin babban Daraktan hukumar Leken Asiri ta kasa NIA.

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa, an dauki wannan mataki ne bisa la’akari da cancanta, musamman ganin cewa Dr Habibat, ‘yar asalin jihar Bauchi, ita ce babbar Sakataren da ta dara saura matsayi, a ofishin Sakataren gwamnatin Tarayyar, yayin da shi kuma Ambasada Arab Yadam, dan asalin jihar Filato, shi ne babba cikin manyan mataimakan babban Daraktan hukumar leken asirin da a ka dakatar.

 

tunein

Tune In