Commissioning of the Upgraded On-Air Studio at Freedom Radio Kano

Tawagar ‘yan dambe ta jihar Kano ta lashe gasar dambe ta kasa

Tawagar ‘yan dambe ta jihar Kano, ta samu damar lashe gasar dambe ta kasa da aka kammala a garin Origi na jihar Ogun, bayan samun nasara kan takwarorin ta  daga sauran wasu jihohin.

Wakilinmu Aminu Halilu Tudun Wada, ya ruwaito mana cewa tawagar ta yan Damben ta samu yawan maki 9,  da tawagar ‘yan wasan dambe biyar daga jihar nan suka sama mata a yayin fafatawar a garin na Origi.

A gasar Jihar Kano, ta samu nasara kan jihar Kaduna, da Katsina, Lagos, Kebbi, Niger da kuma Ogun.

A wani Labarin kuma shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Alhaji Tukur Babangida, ya ce kungiyar ta kammala shirye –shirye don tunkarar gasar kakar wasannin Firimiya ta kasa wato NPFL, mai zuwa.

Tukur Babangida, ya kuma da cewa kungiyar zata yi duk mai yiwuwa don ganin ta dawo da martabar ta da aka santa da shi a da.

A wasannin sada zumunci dake gudana a birnin Kano da kewaye da kuwa:

Kungiyar kwallon kafa ta Elkanemi Warriors, ta sanar da sallamar ‘yan wasa 15, tare da kuma sabunta kwantiragin guda 25.

A wata sanarwa da jami’in yada labaran kungiyar Anthony Obaseki, ya saka wa hannu, ta sanar da cewa yan wasa da kungiyar ta rike sun hada da:

Haka kuma hukumar kwallon Volley ball ta kasa(NVBF) ta gayyaci yan wasa 22 zuwa sansanin horo a Abuja, yan wasan  da suka hada maza da mata, na shirye shiryen wasannin share fagen shiga gasar wasannin kasashen rainon Birtaniya na Commonwealth.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO