Commissioning of the Upgraded On-Air Studio at Freedom Radio Kano

Ana zargin mutane 31 na dauke da cutar mashasharar birrai a jihohi 7 na kasar nan

Cibiyar da ke kula da yadduwar cututtuka ta ce zuwa yanzu ta samu rahoton akalla mutane 31 da ake zargin suna dauke da sabuwar cutar nan ta mashasharar birrai a cikin jihohin kasar nan 7.

A wata sanarwa da shugaban cibiyar Dr. Chikwe Ihekweazu ya fitar tace Jihohin sun hadar da jihar Bayelsa,Rivers,Akwa Ibom, Jihar Lagos,Ogun,da kuma jihar Cross Rivers,sai dai cibiyar ta ce har yanzu bata samu rahoton rasa rai ba.

Wadanda ake zargin suna dauke da cutar ana cigaba da bincike akan su don tabbatar da gano cewa ko cutar ce ko kuwa akasin hakan.

Dr. Ihekweazu yace duk wadanda duk wadanda ake zargin na dauke da cutar na karbar magani sannan kuma suna samun sauki yadda ya kamata,inda kuma yace an dauki na’uin cutar tare da kai shi dakin Gwaje-gwaje na hukumar lafiya ta duniya dake Birnin Dakar na kasar Senegal don tabbatarwa.

A jiya ne dai gwamnatin tarayya ta karyata zargin da ake yi na cewa wai cutar ta barke ne sakamakon wani tallafin magunguna kyauta da ta raba a yankunan da lamarin ya fi kamari.

An dai fara gano bullar cutar na farko ne a jihar Bayelsa,inda aka gano mutum 10 a makon da ya gabata cikin su kuwa har da wani likita.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO