Commissioning of the Upgraded On-Air Studio at Freedom Radio Kano

Hukumar WAEC ta ce na’urorin zamani na saukakawa ayyukan hukumar

Hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandare ta yammacin afurka wato WAEC, ta ce, na’urori na zamani irinsu wayoyi kirar smartphone da kafafen sada zumunta na internet suna matukar saukakawa masu satar jarabawa wajen gudanar da haramtattun ayyukansu.

Shugaban hukumar ta WAEC Iyi Uwadiae ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a wani bangare na shirye-shiryen taron kasa da kasa kan satar jarabawa a Lagos.

Ya ce bincike ya gano cewa hanya daya mafi nagarta da za a magance matsalar satar jarabawa ita ce wayar da kan mutane kan matsalar satar jarabawa a wajen taro irin wadda ke gudana a birnin ta Lagos.

Hukumar ta ce ita ma bata tsaya haka ba ta bullo da sabbin dabaru a dukkanin cibiyoyin rubuta jarabawar ta da ke kasashe mambobin hukumar biyar domin dakile matsalar ta satar jarabawa.

Mr. Iyi Uwadiae, ya kuma buga misali da jarabawar watan Yunin alif dari tara da casa’in da uku (1993), wanda ya ce sakamakon dalibai dubu hamsin da takwas da dari hudu da casa’in da hudu ne kacal aka rike idan aka kwatanta dana bana wanda ya kai dubu dari biyu da goma sha hudu da dari tara da hamsin da biyu (214, 952).

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO