Commissioning of the Upgraded On-Air Studio at Freedom Radio Kano

Shugaba Buhari ya aikewa majalisar Dattawa wasikar amincewa da Aisha Ahmad

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa da majalisar Dattawa wasikar neman amincewa da Aisha Ahmad a matsayin mataimakiyar gwamnan babban bankin kasa na CBN.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da mashawarcin shugaban kasa na musamman kan kafofin yada labarai Femi Adesina ya fitar yau a birnin tarayya Abuja.

Sanarwar ta bayyana cewa ana sa ran Aisha Ahmad zata kama aiki ba tare da bata lokaci ba, da zarar majalisar Dattawan ta amince da ita.

Rahotanni sun bayyana cewa a baya-bayan nan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Aisha Ahmad a matsayin mataimakiyar gwamnan babban bankin kasa na CBN, tare da mikawa majalisar sunan ta domin sahale mata.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO