Commissioning of the Upgraded On-Air Studio at Freedom Radio Kano

dalibai biyar sun bata sakamakon kifewar kwale-kwale a Kaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa akalla dalibai biyar ne suka bata, sakamakon kifewa da su da wani kwale-kwale ya yi a cikin ruwa da tsakar ranar Larabar da ta gabata.

Babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa na jihar Kaduna, Ezekiel Baba-Karik ne ya tabbatar da faruwar al’amarin, lokacin da yake ganawa da manema labarai a jihar ta Kaduna.

Ezekiel ya bayyana cewa daliban nawata makaranta mai zaman kanta ne da ke cikin garin Kaduna, al’amarin ya rutsa da su ne a kan hanyar su ta yawon bude ido da kuma karo ilimi.

A cewar sa an samu nasarar kubutar da hudu daga cikin daliban, inda aka mika su asibitin koyarwa na Barau Dikko domin basu kulawar gaggawa.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO