Commissioning of the Upgraded On-Air Studio at Freedom Radio Kano

Farfesa Yemi Osinbajo ya ce shi ne ya sanya hannun amincewa da fitar da kudaden kwangilar kamfanin NNPC

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce shi ne ya sanya hannu wajen amincewa da batun fitar da kudaden kwangila na kamfanin man fetur na kasar NNPC, kamar yadda kamfanin ya bayyana.

Mataimaki na musamman ga Farfesa Yemi Osinbajo na musamman kan kafofin yada labarai Mista Laolu Akande ne ya bayyana hakan a shafin sa na Twitter.

Akande ya bayyana cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya amince da wannan da batun kwangilar ne don gaggauta kammala ayyukan da ake bukata, tare da biyan basussukan kwangila da ake bin kamfanin.

Laolu Akande ya ce Farfesa Osinbajo ya amince da kwangilar ne a matsayin sa na mukaddashin shugaban kasa, lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi hutun jinya a birnin London.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO