Commissioning of the Upgraded On-Air Studio at Freedom Radio Kano

Yan sanda sun cafke wasu batagarin jami’an tsaro masu satar kayan gwamnati

Yan sanda a jihar Lagos sun damke wasu mutane 11 ciki har da sojoji kasar uku da kuma wani korarren sojan sama bisa zargin satar allunan sanya hasken wutar lantarki na Solar da kudin su ya tasamma miliyan dari mallakin gwamnatin jihar ta Lagos.

Kwamishinan yan sandan jhar ta Legos Imohimi Edgal ne ya bayyana haka ga manema labarai a Larabar da ta gabata inda ya ce dama wadanda ake zargi rundunar yan sandan jhar ta dade ta na neman su kafin daga bisani a damke su.

Imohimi ya ce sojojin guda uku tuni aka aike dasu rundunar sojoji ta tara domin fadada bincike a kansu.

Kwamishinan ya ce barayin sun sayar da kayan da suka sata a bangarori da dama na jihar ta Lagos ga yan kasuwa da dama a yankin Epe Sangotedo Elerngbe da kuma Badagry da kuma wasu sassan kasar.

Haka kuma ya ce an bi diddigin wasu daga cikin wadanda suka sayi kayan a jihar Delta da Anambra da Imo inda kuma aka kama wani a Otal kuma ya amsa cewar ya sayi kayan.

Kwamishinan yan sandan ya ce da zarar an gama bincike kan wadanda ake zargin za’a aike da su kotu domin girbar abinda suka shuka.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO