Tawagar Kano ce ke kan gaba a gasar damben gargajiya da ke gudana a Kaduna

Tawagar Kano a gasar damben gargajiya da ke gudana a Kaduna mai taken: NITRABOL DAMBE CHAMPIONSHIP, ita ce ke kan gaba a jerin jihohin da suka fi samun maki a halin yanzu.

Zuwa yanzu dai Kano ta samu maki goma sha biyu yayin da kuma birnin tarayya Abuja ke biye mata baya da maki tara.

Ogun ce ta biyu da maki hudu sai kuma Jihohin Kebbi da Katsina wadanda suke da maki uku-uku kowannensu.

A fafatwar da aka yi jiya Horon Kande daga Kano ya buge Shagon dan Bature daga Niger yayinda Shagon mai Jeka shi ma Niger ya sha kashi a hannun Shamsu kanin Emi daga Kano, shi kuwa Ali Kanin Bello daga Kano yayi luguden wuta kan dan zabarma daga Niger.

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO