Fashola zai sanya hannu kan gina kamfanin da samar da wutar lantarki MEGAWATTS 3050

A Juma’a ne ake sa ran ministan samar da wutar lantarki ayyuka da gidaje Babatunde Raji Fashola zai sanya hannu kan kwantiragin gina kamfanin samar da wutar lantarki mai karfin MEGAWATTS 3050 a garin Mambila da ke jihar Taraba.

Mukaddashiyar daraktar yada labarai da take kula da bangaren wutar lantarki Misis Etore Thomas ta ce, Babatunde Fashola da dukkannin masu ruwa da tsaki ne za su sanya ido wajen sanya hannu kan kwantiragin.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sanya hannun mukaddashin daraktan kamfanin CGGC wanda shi ne kamfanin da zai yi aikin Mists Zhang Wei.

A cewar sanarwar da zarar kamfanin ya kammala aikin zai samar da megawatts na wutar lantarki dubu uku da hamsin wanda zai taimaka gaya wajen dakile matsalar karancin wutar lantarki a Najeriya.

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO