Jihar Lagos zata rufe wasu kamfanoni da masana’antun a jihar

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Gwamnatin jihar Lagos ta ce daga ranar 20 ga watan nan na Nuwamba zata fara rufe kamfanonin da masana’antun da basa biyan kudaden harajin gwamnati.

Kwamishinan kudi Mr Akinyemi Ashade ne ya fadi hakan yau a jihar ta Lagos, ya ce, wasu bankunan kasuwanci a jihar basa biyan kudaden harajin da ya kamata su bayar fiye da shekaru 10 da suka shude.

Mr Ashade ya kara da cewa gwamnatin ta yi kudirin lalubo dukkanin hanyoyin da doka tayi tanadi domin tabbatar dacewa, kamfanonin sun biya kudin haraji bisa doron doka.

A don haka sai kwamishinan ya shawarci dukkanin kamfanoni da masana’antu su kiyaye da wannan umarni, la’akari da cewa, gwamnati ta yi uzirin daya kamata ga kamfanonin dake biyan kudin haraji rabi da rabi.

Ya ce da kudaden ne gwamnati ke samun sukunin gudanar da ayyukan raya kasa da walwalar Jama’ar jihar.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO