wasu kungiyoyin ma’aikatan manyan makarantun Najeriya zasu fara yajin aiki a yau

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Kungiyar malaman makarantun kwalejojin ilimi da dangogin su NASU, da kuma kungiyar manyan ma’ikatan Asibitocin koyarwa na jami’o’i da na cibiyoyin bincike da kuma kungiyar malaman cibiyoyin bincike na kasa ASURI za su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a yau.

Kungiyoyin sun bayyana cewa dalilin su na tsunduma yajin aikin shi ne rashin girmama yarjejeniyar da suka amince da ita tsakanin su da Gwamnati tun a shekarar 2011.

Da suke zantawa da manema labarai, sakatarorin kungiyar sun bayyana cewa bayan karya Alkawurran da gwamnati ta sha yi musu amma ba ta cikawa, hakan ne ya sanya hakurin su ya kare tare da yanke shawarar tsunduma yajin aikin da suka tabbatar da cewa ba zasu dawo ba har sai gwamnati ta biya musu bukatun nasu.

A jiya ma dai kungiyar malaman makarantun kwalejojin fasaha suka tsunduma yajin aiki wanda suka ce baza su dawo ba har sai gwamnati ta biya musu bukatun su.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO