Rundunar yan sandan jihar Ebonyi ta gargadi mambobin kungiyar IPOB

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Rundunar yan sandan jihar Ebonyi ta gargadi mambobin kungiyar IPOB dake rajin kafa yantacciyar kasar Biafra da sauran jam’iyyun siyasa kan tada hatsaniya yayin ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai jihar a yau.

Kwamishinan yan sandan jihar ta Ebonyi Titus Lamorde, yayi wannan gargadin yayin wata zantawa da manema labarai a babban birnin jihar Abakaliki.

Ya ce rundunar a shirye take ta sanya kafar wando daya da duk wani mutum ko wata kungiya dake shirin tada zaune tsaye a yayin ziyarar da shugaban kasa zai kai jihar yau,tare da tabbatar da tsaro.

A cewar Lamorde ya bayyana cewa jami’an rundunar a shirye suke da su yi kyakyawar mu’amala da al’umma yayin ziyarar ta shugaban kasa,amma kuma hakan ba zai hana su tabbatar da doka da oda ba.

Ya kuma ce matsayin su na jami’an tsaro ba zasu yarda su shigar da harkokin siyasa cikin aikin su ba, amma ziyarar ta shugaban kasa abu ne da zai kawo cigaba a jihar duba da irin abubuwan da shugaban kasa zai kadammar a jihar.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO