Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta gurfanar da gwamnatin jihar Kaduna a gaban Kotun ma’aikata

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta Najeriya, ta gurfanar da gwamnatin jihar Kaduna gaban Kotun ma’aikata da ke Abuja, tana mai kalubalantar matakin da gwamnatin jihar ta dauka na dai-daita yawan ma’aikatan kananan hukumomi a duk kananan hukumomin jihar.

A cikin takardar karar da suka shigar gaban kotun ta hannun lauyan kungiyar Femi Aborisade, tace Gwamnan bashi da ikon yin hakan a matsayin doka.

Cikin wadanda kungiyar ta gurfanar gaban kotun akwai Gwamnan jihar ta Kaduna da kuma shugaban majalisar dokokin jihar da Antoni Janar kuma Kwamishinan shari’a na jihar.

Sauran wadanda suka gurfanar gaban kotun sun hadar da Kwamishinan kananan hukumomi na jihar, da shugaban ma’aikata na jihar da hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomi da kuma gwamnatin jihar ta Kaduna.

Kungiyar dai na bukatar kotu ta haramtawa gwamnatin jihar daukar wannan mataki inda suka ce bashi da wani hurumi a dokar kasar nan.

Haka kuma kungiyar ta aike da wata takarda ga Ministan samar da ayyukan yi Chris Ngige, suna masu bukatar ya shiga tsakani.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO