Commissioning of the Upgraded On-Air Studio at Freedom Radio Kano

Mai horas da ‘yan wasan Super Eagles ya mika tsare-tsarensa na halartar gasar cin kofin duniya na shekarar badi

Mai horas da ‘yan wasan Super Eagles Gernot Rohr, ya mikawa hukumar kwallon kafa ta kasa NFF tsare-tsarensa na halartar gasar cin kofin duniya wanda za a yi a kasar Rasha a badi.

Shugaban kwamitin kwararru na hukumar ta NFF Alhaji Ahmed Yusuf Fresh ya tabbatar da cewa Bajamushen ya mika irin tsare-tsarensa kan gasar da za’a yi a kasar Rasha.

Yusuf Ahmed Fresh ya ce, cikin tsare-tsaren da kocin na Super Eagles ya gabatar sun hada da: kasa da kuma garin da ‘yan wasan na Super Eagles zasu yi sansani kafin tafiyar su kasar ta Rasha da kuma adadin wasannin sada zumunci da zasu yi.

A watan jiya ne dai Super Eagles ta samu tikitin halartar gasar ta cin kofin duniya wanda za’a yi a kasar Rasha a badi bayan da ta kammala dukkannin wasannin ta 6 a rukunin ‘ B ’ wanda ke kunshe da kasashen Kamaru da Aljeriya da kuma Zambia ba tare da an samu galaba a kanta ba.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO