Wata kotun kasar Italiya ta daure tsohon dan wasan kwallon kafa Robinho na tsawon shekaru 9

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Wata kotu a kasar Italiya ta daure tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da Manchester city Robinho har na tsawon shekaru tara.

Kotun dai ta ce Robinho mai shekaru 33 dan kasar Brazil yana daya daga  cikin gungun  mutane da suka yi fyade ga wata mata a birnin Milan a shekarar 2013.

ita ma wata kotu a kasar Afirka ta kudu ta kara wa’adin zama gidan yari ga tsohon zakaran gasar Olympics ta Nakasassu Oscar Pistorius daga shekaru 6 zuwa 13 da wata 5 sakamakon kamashi da laifin kashe budurwarsa.

Tun da fari dai wata kotu ce ta daure Pistorius Shekaru 6 hukuncin da iyalan budurwar tasa da kuma masu gabatar da kara suka ce an yi mishi sassauci sosai.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO