Wata kotun tarayya a Lagos ta kwace wasu manyan gine-gine biyu mallakin Diezani

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Wata kotun tarayya a Jihar Lagos ta kwace wasu manyan gine-gine guda biyu mallakin tsohuwar Ministar albarkatun man fetur Diezani Alison-Madueke tare da mikawa gwamnatin tarayya.

Mai Shari’a Mojisola Olatoregun ta zartas da kwarya-karyar hukuncin kan ginin Penthouse da ke rukunin gidajen Bella Vista da kuma wani makamancinsa a rukunin gidaje na Admiralty, dukkanninsu a Banana Island da ke Ikoyi.

Gine-ginen za su ci gaba da kasancewa a hannun gwamnatin tarayya har sai a EFCC ta kammala binciken yadda ta mallaki gidajen.

Wannan hukunci na zuwa ne watanni kadan bayan da wata kotun ta yanke hukuncin kwace wani katafaren gini da kudinsa ya tasanma sama da Dala miliyan 37 mallakin Diezani din tare da mikawa gwamnatin tarayya kacokan.

Haka zalika wata kotun ta yanke hukuncin kwace gidaje 56 mallakin Diezani din da kudinsu ya kai Naira Biliyan 3, da aka yi zargin ta saye su ne tsakanin shekarar 2011 zuwa 2013.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO