Fiye da kananan yara 37,000 ne suka kamu da kwayar cutar ta HIV a shekarar 2016-UNICEF

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, ya ce; akalla kananan yara ‘yan kasa da shekaru goma sha hudu da dubu dari biyu da saba’in ne ke dauke da kwayar cutar HIV mai karya garkuwar jiki a cikin shekarar da ta wuce ta 2016.

A cewar asusun wannan adadin ya kai kaso hamsin na kafatanin yaran yammacin afurka da ke dauke da cuta mai karya garkuwar jiki wanda yawansu ya kai dubu dari biyar da arba’in.

Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniyar UNICEF ya kuma ce a cikin shekarar ta 2016 yara akalla 37,000 ne suka kamu da kwayar cutar ta HIV wanda ya fi kaso sittin na adadin yara da suka kamu da cutar a yankin yammacin da kuma tsakiyar afurka wanda ya kai dubu 60,000.

A cewar rahoton yammacin da tsakiyar afurka sune yankuna da suka fi karancin magunguna rage karfin ciwon da kuma ba da kulawa ga masu dauke da kwayar cutar ta HIV.

Babbar daraktar asusun na UNICEF mai kula da yankin yammaci da tsakiyar afurka Ms Marie-Pierre Poirier  ta cikin rahoton da asusun ya fitar a jiya Talata, ta bukaci da shugabannin a yankin yammacin da tsakiyar Afurka da su kara kaimi wajen dakile yaduwar cutar tsakanin kananan yara.

 

Ms Marie Pierre-Poirier ta cikin rahoton ta kuma bayyana cewa yara hudu cikin biyar a yankin yammaci da tsakiyar afurka ba sa samun cikakken kulawa ta musamman wajen samar musu da magungunan rage radadin cutar.

Asusun na UNICEF ya kara da cewa mutuwar yara da shekarun-su suka fara daga 15 zuwa 19 ya yi matukar karuwa a ‘yan shekarun nan a don haka wajibi ne ga mahukunta su tashi tsaye wajen yakar matsalolin da ke janyo koma baya ga shirin dakile yaduwar cutar.

Ta cikin rahoton na UNICEF dai ya nuna cewa kaso ashirin da daya kacal cikin dari na adadin yara da yawansu suka kai 540,000 wadanda shekarunsu suka fara daga daya zuwa 14 ne a shekarar 2016 suke samun magunguna na rage radadin cutar wanda ya nuna cewa yankunan biyu na afurka sune koma baya a duniya baki daya.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO