Kotun kolin ta sanya ranar 2 ga wata don hunkunci kan karar da Sambo dasuki ya yi na tsare shi

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Kotun kolin Najeriya ta saka ranar 2 ga watan Maris na shekarar 2018 domin yanke hunkunci kan karar da tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Kanal Sambo dasuki ya yi na kalubalantar tsare shi da ake yi har illa Masha Allahu.

Alkalan kotun koli su biyar da suka yi zaman wanda mai shari’a Dattijo Muhammad ya jagoranta  sun sanya ranar ne bayan lauyoyi masu kare mai kara da sauran sun bayar da bayanan su.

Shi dai tsohon mai baiwa shugaban kasar shawara Sambo Dasuki tun a ranar 16 ga watan Yunin shekara ta 2016, ne kotun daukaka kara dake Abuja ta ki yarda da rokon da Sambo Dasukin ya yi mata na a sake shi bayan wasu kotuna sun bayar da belinsa bisa zargin da ake masa.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon mai bawa tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan din shawara a harkokin tsaro kanal Sambo Dasuki na fuskantar shari’a ne saboda zargin yin almundahana da kudi fiye da dala biliyan 2 wadanda aka ware domin sayan makamai na yaki da yan Boko Haram.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO