Rundunar sojin Najeriya ta yi sauyin wurin aiki ga kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Rundunar sojin Najeriya ta yi sauyin wurin aiki ga kwamanda mai kula da rundunar ”Operation Lafiya Dole” Manjo Janar Ibrahim Attahiru tare da maye gurbinsa da Manjo Janar Rogers Nicholas.

Cire Manjo Janar Ibrahim Attahiru ana ganin ya Biyu bayan wani mummunan hari da Yan tada kayar baya su ka kai a garin Biyu na jihar Borno inda mutane 18 suka rasa rayukansu, mutum 52 kuma suka samu manyan raununnuka.

A sati biyu da suka gabata ne dai babban hafsan tsaron Najeriya Janar Gabriel Abayomi Olanisakin ya kai ziyarar bazata ga cibiyar yaki da yan tada kayar baya shi kadai, ba tare da sauran hafsoshin soja ba, sannan ya tattauna cikin sirri da tsohon kwamandan na ”Operation Lafiya Dole” Manjo Janar Ibrahim Attrahir.

Shi dai sabon kwamandan na operation lafiya dole Manjo Janar Rogers Nicholas , shine tsohon mai kula da harkokin gudanarwa da al’amuran sojoji na hedikwatar rundunar sojojin kasa.

Shi kuma Manjo Janar Ibrahim Attahiru anyi masa sauyin gurin aiki zuwa hedikwatar sojan kasa dake Abuja.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO