Jihar Ondo za ta baiwa kungiyar Sunshine stars kudaden tafiya gasar Firimiya

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Gwamnatin jihar Ondo ta ce ma’aikatar matasa da wasanni ta jihar za ta baiwa kungiyar kwallon kafa ta Sunshine stars kudade da za su yi amfani da su yayin wakiltar jihar a gasar Firimiya ta kasa a kakar shekara mai zuwa.

Gwamna jihar Ondo Rotimi Akeredolu na bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a garin Akure babban birnin jihar.

‘yan wasan kungiyar ta Sun shine stars dai na bin bashin kudaden alawus-alawus din din su na kakar wannin ta shekarar 2016/2017, inda gwamnan yayi alwashin baiwa kungiyar kudaden na su da suka makale.

Gasar dai za’a fara ta ranar 14 ga watan Junairun badi, kuma Kungiyar ta sunshine stars za su fara wasan su na gasar Firimiya ta kasa ta bana da zasu fara da kungiyar Heartland ta jihar Owerri

A nan gida kano kuma kyfatin kungiyar wasan langa ta Jarumai Badamasi Murtala ya ce duk da rashin nasarar lashe kofin da kungiyar sa tayi wasan langar da ta gabata za su ci gaba da kara karbar horo don ganin sun lashe gasar da za su fafata a nan gaba.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO