Commissioning of the Upgraded On-Air Studio at Freedom Radio Kano

Hukumar NFF ta shirya wa kungiyar Super Eagles wasannin sada zumunci

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta shirya wa kungiyar Super Eagles wasannin sada zumunci guda hudu, don karawa ‘yan wasan karsashin tunkarar gasar cin kofin Duniya ta badi da za ta gudana a kasar Rasha.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Amaju Pinnick ne ya tabbatar da hakan a jiya a filin wasa na Agege da ke Jihar Lagos.

Amaju Pinnick ya ce kungiyar ta Super Eagles za ta buga wasan farko ranar 2 ga watan Janairu mai kamawa da takwarorinsu na kasar Ingila, a filin wasan na Wembley da ke London.

Ya kuma kara da cewa Super Eagles din za ta kara yin wasan ranar 27 ga watan Mayun badin, sai dai ya zuwa yanzu ba a bayyana sunan kasar da za su kara da ita ba.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO