Bankin raya Afrika ya musanta rade-raden cewar ya baiwa kasarnan rance

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Bankin raya afurka ya musanta rade-raden da ke yawo a kafofin yada labaran kasar nan cewa ya fasa baiwa kasar nan rancen dala miliyan dari shida da ya alkawarta tun da fari.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babbar jami’ar yada labaran bankin a kasar nan Fatima Alkali.

Sanarwar ta ruwaito mataimakin shugaban bankin mai kula da sashen samar da wutar lantarki da makamashi da kuma yanayi Amadou Hott; na musanta zargin.

A cewar Fatima Alkali ta cikin sanarwar, babu kanshin gaskiya cikin lamarin.

Sanarwar ta kara da cewa bankin raya afurka a shirye yake ya yi aiki tare da hukumomin kasar nan domin farfado da tattalin arzikin ta.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO