Hukumar tsaro ta Civil Defence ta gargadi dillalan man fetur kan boye man da wasu daga cikinsu ke yi

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Hukumar tsaro ta Civil Defence ta gargadi dillalan man fetur da su kuka da kan su kan boye man fetur da kuma karkatar da shi wanda a ka dauko shi musammam domin al’ummar Jihar Yobe.

Babban kwamandan hukumar shiyyar jihar ta Yobe Ayinla Taiye Olowo shi ne ya yi wannan gargadi yayin da yake zantawa da manema labarai a jiya Alhamis a garin Damaturu, inda ya ce duk wanda aka kama daga cikin su zai fuskanci fushin hukumar.

Ya ce matsalolin da ake ta samu na boye mai tare da karkatar dashi ya janyo matsalar karancin man da ake ta fama da shi lamarin da ya jefa al’umma cikin mawuyacin hali.

Haka kuma ya ce hukumar ta na sane da wasu gidajen mai da ke sayar da mai sama da farashin gwamnati cikin dare inda ya ce jami’an hukumar za su ci gaba da sanya idanu domin damke wadan da ke da wannan mummunar ta’ada.

Ya kuma bukaci al’umma a jihar ta Yobe da su kai rahoton duk wani gidan mai da yake boye mai ko kuma sayar da shi ba bisa ka’ida ba ga hukumar inda tayi alkawarin za ta hada hannu a da Jama’a wajen magance matsalar.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO