Masarautar Kano ta bayyana gamsuwarta kan makarantar Gwadabe mai tasa wajen tafiyar da harkar koyo da koyarwa

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Majalisar masarautar Kano ta ce ta gamsu da yadda makarantar Gwadabe mai tasa Al’islamiya dake unguwar ‘yar mai shinkafi ke tafiyar da harkar koyo da koyarwar ta, inda ta bukaci sauran makarantu da su yi koyi da irin tsarin koyarwar na makarantar ta Gwadabe Maitasa.

Wamban Kano Hakimin cikin birni Alhaji Aminu Ado Bayero ne ya bayyana haka yayin bikin saukar daliban makarantar karo na 25 da kuma karrama wasu fitattun mutane da 25 da suka baiwa makarantar gudun mawa da ya gudana yau a harabar makarantar da ke unguwar yar mai shin kafi anan birnin Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce makarantar ta Gwadabe mai tasa ta dade tana bada gudun mawa a cikin al’umma wajen ilimantar da al’umma da ciyar da su gaba.

Da yake nasa jawabin shugaban makarantar Malam Usman Kabir Umar wanda aka fi sani da malam kuliya ya jaddada kudirin sa na ci gaba da bayar da gudunmawa ta bangaren ci gaban maakranta da ganin matsa ma su tasowa sun sami ilimi nai nagarta.

A nasa jawabin Alhaji Abba Mukhtar Muhammad koka wa ya yi kan yadda halayyar al’umma ta ke wajen rashin baiwa karatun addini muhimmanci wanda shi ne abin da ya rage wa wannan al’umma wajen gina tarbiyyar ta.

Kimanin dalibai dari da ashirin da bakwai ne suka yi sauka yau, yayin da aka karrama wasu mutane 25 da suka hadar da marigayi mai Martaba sarkin Kano Alhaji Ado Bayero Da sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussaini Adamu da kuma Tsohon mataimakin gwamnan kano Alhaji Ahmad Usman.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO