Rundunar sojin Najeriya ta kashe mayakan Boko-haram 23 yayin wata arangama

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe mayakan Boko-haram guda ashirin da uku yayin wani batakashi da suka yi a yankin tabkin Chadi.

Daraktan yada labarai na rundunar,burgediya Janar Texas Chukwu ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a garin Maiduguri.

Sanarwar ta ce, rundunar ta kuma samu nasarar kwato makamai da dama daga hannun ‘yan ta’addar.

Haka zalika burgediya Janar Texas Chukwu ta cikin sanarwar dai, ya kuma ce; ba ya ga wadanda suka rasa rayukansu mayakan na Boko-haram da dama kuma sun tsere da munanan raunuka.

A cewar sanarwar dakarun bataliya ta 153 tare da goyon bayan sojojin Kamaru ne suka yi kofar rago ga mayakan na Boko-haram.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO