Majalisar zartawa gwamnatin tarayya ta amince da fitar da fiye da naira biliyan 185

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Majalisar zartarwar gwamnatin tarayya ta amince da fitar da naira biliyan 185 da miliyan 272 domin ayyuakan gyara da kuma gina sabbin hanyoyi goma sha hudu a fadin kasar nan.

 

Mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan kafafen yada labarai Femi Adesina ne ya sanar da hakan ga manema labarai jim bayan kammala zaman majalisar zartarwar na jiya.

 

Ya kuma bayyana wasu daga cikin hanyoyin da za a gina da kuma yiwa gyara da suka hadar da hanyar da ta tashi daga Goza zuwa Dambowa zuwa Goniri zuwa Ngamdu dake jihar Yobe da kuma Borno.

 

Sai kuma hanyar da ta tashi daga Mayo Balwa zuwa Jada zuwa Ganye zuwa Torngo da ke jihar Adamawa, sai kuma hanyar da ta tashi daga Ado zuwa Ifaki zuwa Otun da ke kan iyakar jihar Kwara da kuma Ekiti

 

Haka kuma ya ce an kammala dukkanin wasu shirye-shirye domin sanya hannu akan kasafin kudin wannan shekarar da shugaban kasa zai yi nan da yan kwanaki masu zuwa

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO