Rundunar sojin kasar na ta aike da karin jirage biyu jihar Zamfara

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Rundunar sojin saman kasar nan ta aike da karin jirage biyu ga rundunar ta da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar Zamfara karkashin shirin kai daukin gaggawa ga yankunan da ke fuskantar barazanar tsaro a jihar Zamfara.

 

Matakin rundunar na zuwa ne a dai dai lokacin da yawan ‘yan gudun hijira da suka kauracewa kauyukan su sakamakon matsalar tsaro a sassan jihar ta Zamfara ke tasamma dubu 10.

 

Kwamandan runduna ta 207 da ke yaki da ayyukan ta’addanci a Zamfara Kaftin Caleb Olayera ya ce ta hanyar aiki da jiragen Shalkwaftar ne za a iya kai daukin gaggawa ga yankunan da ke fuskantar hare-haren ‘yan bindiga.

 

A cewar kwamandan maimakon jiran karin dakaru daga jihohin Kano da Bauchi yanzu jiragen su za su fara tashi daga birnin Gusau don kai dauki a sassan da ke cikin matsala ta hanyar shawagi a sararin samaniya.

 

Rundunar dai ta samu karin akalla jirage biyu daga shalkwatar ta ta kasa don fatattakar ‘yan bindigar da ke barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar ta Zamfara.

 

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO