An yanke wa gidan gwamnatin jihar Imo wutar lantarki

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Kamfanin rarraba wutar lantarki na shiyyar Enugu ya yanke wutar gidan gwamnatin Jihar Imo tare da Sakatariyar Jihar saboda bashin naira miliyan dari biyu da yake bi.

Mai magana da yawun kamfanin Emeka Ezah ne ya bayyana hakan ga manema labarai, ya na mai cewa ba san ran su bane maganar ta je kafofin yada labarai, sai dai dan barazanar ruguje ginin kamfanin da gwamnatin jihar Imo tai musu.

Emeka ya kuma ce ana ta kokarin yadda za’a shawo kan matsalar har gwamnatin ta biya kudaden.

A ta bakin Emeka kin biyan kudin wutar da masu ruwa da tsaki ke yi, ka iya haifar da matsaloli tsakanin kamfanin da talakawan gari.

 

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO