Hukumar WAEC ta saki sakamakon jarrabawar watan Mayu da Yuni

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Hukumar WAEC da ke shirya jarrabawar kammala karatun sakandire ta yammacin Afurka, ta saki sakamakon jarrabawar bana na watan Mayu da Yuni.

Da yake sanar da sakin sakamakon, shugaban hukumar mai kula da kasar nan Mr. Olu Adenipekun, ya ce cikin dalibai miliyan daya da dubu dari biyar da saba’in da biyu da su ka rubuta jarrabawar a bana, dubu dari bakwai da tamanin da shida da goma sha shida sun samu sakamako mai kyau wato credit biyar zuwa sama ciki kuwa har da darusan lissafi da turanci.

Ya kuma shawarci wadanda suka rubuta jarrabawar kuma suka tabbatar da cewa sun biya kudin su lakadan, da su ziyarci shafin hukumar a yanar gizo domin duba sakamakon su.

A cewar sa sakamakon na bana, ya nuna cewa kaso arba’in da tara da digo casa’in d takwas sun samu sakamako mai kyau

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO