Commissioning of the Upgraded On-Air Studio at Freedom Radio Kano

Kaso daya cikin dari ke samun gurbin karatu a jami’oin kasar nan

Hukumar kula da jami’oi ta kasa NUC, ta ce; kaso daya cikin dari na adadin al’ummar kasar nan ne kawai suka iya samun gurbi a jami’oin kasar nan guda dari da sittin da hudu.

 

Shugaban hukumar ta NUC farfesa Abubakar Rashid ne ya bayyana haka, yayin zantawa da manema labarai jiya a Abuja.

 

Ya ce, jami’oi masu zaman kansu guda saba’in da biyar da kasar nan ke da ita, sun iya daukar kaso biyar da digo talatin da daya cikin dari ne kacal na daliban da ke jami’oin kasar nan.

 

Farfesa Abubakar Rashid, ya kuma bukaci da a kara adadin jami’oin tare da bude sababbi.

 

Shugaban hukumar ta NUC, ya ce; akwai damuwa matuka ganin cewa a yanzu adadin daliban da suka samu gurbi a jami’oin kasar nan su miliyan daya da dubu dari tara da sittin da daya ne kacal.

 

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO