Rundunar sojin Najeriya ta kashe mayakan Boko haram 14 a titin Pulka zuwa Gwoza

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta samu nasarar kashe mayakan Boko haram guda goma sha hudu wadanda suka sace wata motar bus dauke da fasinjoji akan titin Pulka zuwa Gwoza a baya-bayan nan.

Haka zalika sojojin sun kuma samu nasarar ceto mutanen da ‘yan boko haram din suka sace su ashirin da uku yayin wani samame da suka kai kan maboyar su.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar Burgediya Janar Texas Chukwu.

Sanarwar ta ce, rundunar bataliya ta 192 ta Operation lafiya dole ce tare da hadin gwiwar sojojin sakai na civilian JTF da suka kai samamen.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO