Shugaba Buhari ya mika da sakon ta’aziyya ga gwamnati da a’ummar jihar Nassarawa bisa ga gobarar iskar gas

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika da sakon ta’aziyar sa ga gwamnati da al’ummar jihar Nassarawa bisa ga gobarar da ta tashi a wata cibiyar sarrafa iskar gas da ke daf da wani gidan mai da ke garin Lafiya a jihar ta Nassarawa wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.

Sanarwar ta ruwaito shugaba Buhari na nuna damuwar sa matuka kan irin adadin mutanen da suka rasa rayukan su a dalilin hatsarin, inda mutane goma suka mutu wasu talatin suka jikkata ba ya ga motoci da shaguna da dama da suka kone.

Shugaba Buhari ta cikin sanarwar dai ya kuma mika sakon ta’aziyar sa ga iyalai da kuma ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukan su.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO