Hukumar INEC:Jam’iyyun su kaucewa dabi’ar fara yakin neman zabe

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gargadi ‘yan siyasa tare da jam’iyyun da su kaucewa dabi’ar fara yakin neman zabe tun kafin lokaci ya yi.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya sanar da hakan a jiya Litinin lokacin da ya ke gabatar da jawabi a taron bitar da kungiyar kasashe rainon Ingila ta shirya tare da hadin gwiwar INEC, don wayar da kan kwararru a fannin harkokin zabe shiyyar Afirka.

Farfesa Yakubu ya ce sashe na 99(1) na kundin tsarin mulkin kasar nan ya haramtawa ‘yan siyasa da m jam’iyyun siyasa tsunduma yakin neman zabe har sai saura kwanaki 90 a gudanar da zabe.

Hukumar zaben ta yi tanadin cewa za a fara yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisun Kasa a ranar 18 ga watan Nuwamba mai kamawa, yayin da kuma za a fara yakin zaben gwamnoni da na ‘yan Majalisun Jihohi a ranar 1 ga watan Disamba mai zuwa.

Gargadin na INEC na zuwa ne bayan kammala zaben fidda gwani na shugaban kasa da gwamnoni a jam’iyyun siyasar kasar nan, har ma Farfesa Mahmoud Yakubu ya ja hankalin ‘yan siyasar kan su kaucewa take doka

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO