Za’a kammala aikin titan Badin ruwa Lagos a shekara ta 2021

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Kamfanin da ke aikin gina babbar hanyar  garin Badin zuwa Lagos ya ba da tabbacin kammala aikin Titin daga nan zuwa shekarar 2021.

Babban jami’in gudanawar Kamfanin Thamm Olaf ne ya shaida hakan lokacin da yake bada ba’asi a gaban Kwamitin ayyuka na Majalisar Dattijai a jiya Lahadi.

Ya kara da cewa sun gaza kammala aikin a shekarar da ta gabata kamar yadda aka tsara sakamakon karancin kudade, da kuma sake fadada aikin da aka yi.

Yayin ziyarar gani da ido da Kwamitin ya kai wuraren da ake aikin a Jihar Lagos karkashin shugabansa Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, ya bayyana rashin jin dadinsa duk kuwa da makudan kudaden da gwamnatin ta narka cikin aikin ginin Titin.

Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya shaidawa manema labarai cewa Kamfanin da ke aikin wurin ajiye mayan Motoci na Tin Can Island ya sanar da su cewa zai kammala a cikin Disamba mai kamawa, don saukaka cunkokson ababen hawa da ake samu.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO