Wasu jihohin Najeriya za su yi asarar Dala Miliyan 700 na kudaden tallafi daga bankin CBN

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Wasu daga cikin jihohin kasar nan ba za su sami Dala Miliyan dari 700 na kudaden tallafi daga bankin kasar nan in har suka gaza buga kasafin kudin su na badi a kafar Internet daga nan zuwa watan Fabarerun badi.

Babban daraktan hukumar hadi gwiwa na gwamnatoci na jihar Niger Alhaji Sirajo Sai’d ya bayyana hakan a yayin taron hadin gwaiwa da hukumar da kuma kungiyoyin kishin al’umma da aka yi a birnin Minnan jihar Naija.

A cewar Ahaji Sirajo Sa’id ya ce tallafin kudaden wanda zai zo karkashin shirin fayyace gaskiya kan tattalin arziki da kudi da kuma dorewar cigaban ayyukan wanda gwamnatin tarayya ta karba a madadin gwamnatocin jihohin kasar nan.

Babban darktan hukumar ta hadin gwiwar gwamnatocin na jihar Niger ya kara da cewar, makasudun baiwa gwamnatocin tallafin kudaden da bankin duniya zata yi shi ne don tabbatar da ayyukan al’umma da tsage gaskiya wajen kashe kudade don cigaban ‘yan Najeriya.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO